Hebrews 11

1Bangaskiya ita ce tabbatawar al’muran da muke begensu. Ita ce tabbatawar al’amuran da idanu basu gani. 2Domin ta wurin ta ne kakanninmu suka sami yardar Allah. 3Ta wurin ta ne aka hallicci duniya da umarnin Allah, har ma abubuwan da ake gani ba’a yi su daga abubuwan da suka kasance ba.

4Ta dalilin bangaskiya ne Habila ya mikawa Allah hadaya da ta fi dacewa fiye da ta Kayinu. Don haka ne kuma aka yaba masa akan cewa shi adali ne. Ya sami yardar Allah sabili da sadakarsa da ya bayar. Don haka kuma, harwayau Habila yana magana, ko da shike ya rigaya ya mutu.

5Ta dalilin bangaskiya aka dauki Anuhu zuwa sama domin kar ya ga mutuwa. “Ba a same shi ba kuwa, domin Allah ya dauke shi.” Kamin a dauke shi an shaida da cewa ya faranta wa Allah zuciya. 6Zai yi wuya matuka a faranta wa Allah zuciya in ba tare da bangaskiya ba. Domin ya kamata dukkan wanda zai zo ga Allah, tilas ne ya bada gaskiya da kasancewar sa, kuma shi mai sakamako ne ga dukkan masu nemansa.

7Ta dalilin bangaskiya Nuhu, ya karbi sako daga Allah akan al’amuran da ba’a gani ba, ta wurin girmamawa da rawar jiki. ya gina jirgin ruwa domin ya ceci iyalan sa. Dalilin haka kwa, Allah ya hallakar da duniya, Nuhu kwa ya gaji adalci wadda ke bisa ga bangaskiya.

8Ta dalilin bangaskiya ne Ibrahim, sa’an da aka kira shi, ya yi biyayya sai ya tafi wurin da zai karba a matsayin gado. Ya kwa fita bai ma san inda za shi ba. 9Ta dalilin bangaskiya kuma ya zauna bare a kasar alkawari. Ya yi zama cikin Alfarwa tare da Ishaku da Yakubu, magadan alkawari guda tare da shi. 10Domin yana hangar birnin da ke da tushi, Birnin da mai zaiyanar sa da ginin sa shine Allah.

11Ta dalilin bangaskiya, Ibrahim ya sami haihuwa ko da shike shi da matarsa Saratu sun yi nisa a cikin shekaru, kuma Saratu bakarariya ce, ta kuma wuce lokacin haihuwa. Tun da shike sun amince da wanda ya yi musu alkawari mai aminci ne. 12Sabo da haka, ta wurin mutumin nan daya, wanda ya ke kamar matacce ne, aka haifi zuriya mai dimbin yawa, su ka yawaita kamar taurari a sama kamar yashi a bakin teku, wanda ba shi kidayuwa.

13Dukkan su kuwa suka mutu a cikin bangaskiya ba tare da sun karbi alkawarin ba. Maimakon haka, sun hango, kuma sun marabcesu daga nesa, sai suka amince su baki ne kuma matafiya ne a duniya. 14Gama wadanda suka yi furci haka sun nuna a fili cewa suna bidar kasa ta kansu.

15Da kamar suna tunanin kasar da suka fita daga ciki, da sun sa mi damar komawa. 16Amma kamar yadda yake, sun bukaci kasa mafi dacewa, wato, wadda take a sama. Saboda haka ne Allah bai ji kunyar a kira shi Allahnsu ba, da shike ya shirya birni dominsu.

17Ta dalilin bangaskiya ne Ibrahim, sa’adda aka yi masa gwaji, akan ya mika Ishaku dansa hadaya. 18Shi ne kuwa makadaicin dansa, wanda aka yi alkawari da cewa, “Ta wurinsa ne za a kira zuriyarka.” 19Ibrahim ya yi tunani da cewa Allah na da ikon tada Ishaku ko daga cikin matattu ma, haka kuwa yake a misalce, daga matattun ne ya sake karbarsa.

20Ta dalilin bangaskiya ne kuma Ishaku ya albarkaci Yakubu da Isuwa game da abubuwan da ke zuwa a gaba. 21Dalilin bangaskiya ne Yakubu, sa’adda yake bakin mutuwa, ya albarkaci ‘ya’yan Yusufu dukkansu biyu. Yakubu ya yi ibada, yana tokare a kan sandarsa. 22Ta dalilin bangaskiya Yusufu, sa’adda karshensa ya kusa, ya yi magana game da fitar ‘ya’yan Isra’ila daga Masar har ya umarce su game da kasussuwansa.

23Ta dalilin bangaskiya Musa, sa’adda aka haife shi, iyayensa suka ‘boye shi kimanin watanni uku domin kyakkyawan yaro ne shi, kuma basu ji tsoron dokar sarki ba. 24Ta dalilin bangaskiya ne kuma Musa, sa’adda ya girma, yaki a kira shi ‘dan diyar Fir’auna. 25A maimakon haka, ya amince ya sha azaba tare da jama’ar Allah, a kan shagali da annashuwar zunubi na karamin lokaci. 26Ya fahimci cewa wulakanci domin bin Almasihu babbar wadata ce fiye da dukiyar Masar. Gama ya kafa idanunsa a kan sakamakon da ke gaba.

27Ta dalilin bangaskiya Musa ya bar Masar. Bai ji tsoron fushin sarki ba, ya jure kamar yana ganin wannan da ba a iya ganinsa 28Ta dalilin bangaskiya ya yi idin ketarewa da kuma yayyafa jini, domin kada mai hallaka ‘ya’yan fari ya taba ‘ya’yan fari na Isra’ila.`

29Ta dalilin bangaskiya suka haye baharmaliya kamar bushashiyar kasa. Sa’adda Masarawa su ka yi kokarin hayewa, bahar din ta hadiye su. 30Ta dalilin bangaskiya ganuwar Yeriko ta fadi, bayan sun kewaya ta har kwana bakwai. 31Ta dalilin bangaskiya Rahab karuwan nan bata hallaka tare da marasa biyayya ba, don ta saukar da masu leken asirin kasa a gidanta, ta kuma sallame su lafiya.

32Me kuma za mu ce? Gama lokaci zai kasa mini idan zan yi magana game da Gidiyon, Barak, Samson, Yefta, Dauda, Sama’ila, da annabawa. 33Ta dalilin bangaskiya suka ci nasara kan kasashe, suka yi aikin adalci, sa’annan suka karbi alkawura. Suka rufe bakin zakuna, 34suka kashe karfin wuta, suka tsira daga bakin takobi, suka sami warkaswa daga cutattuka, suka zama jarumawan yaki, sa’annan suka ci nasara akan rundunar sojojin al’ummai.

35Mata kuwa suka karbi matattunsu da aka tayar daga mutuwa. Aka azabtar da wadansu, ba su nemi yancin kansu ba, domin suna begen tashi daga mattatu. 36Wadansu kuwa suka sha ba’a da duka da bulala, har ma da sarka da kurkuku. 37A ka jejjefe su. Aka tsaga su kashi biyu da zarto. A ka karkashe su da takobi. Su na yawo sanye da buzun tumakai da na awaki, suka yi hijira, suka takura, suka wulakantu. 38Duniya ma ba ta dauke su a matsayin komai ba. Suka yi ta yawo a jazza, da duwatsu, da kogwanni, da kuma ramummuka.

39Ko da yake mutanen nan amintattun Allah ne domin bangaskiyarsu, basu karbi cikar alkawarin ba tukunna. Domin Allah ya shirya mana wani abu mafi kyau ba kuwa za su kammala ba sai tare da mu.

40

Copyright information for HauULB